Yadda na hada dangantaka da Aliko Dangote shekarun baya – Inji Bill Gates

Yadda na hada dangantaka da Aliko Dangote shekarun baya – Inji Bill Gates

Da aka tambayi Bill Gates ko ya taba haduwa da wani mutum a Duniya wanda daga fara magana da shi sai ya ji kamar ka da su rabu, sai yace wannan ya faru a lokacin da ya ga Aliko Dangote.

Bill Gates ya ce shekaru da-dama da su ka wuce ya fara haduwa da Aliko Dangote a wajen wani taro da wani Amininsu ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin Attajiran Duniyar sun zauna wuri guda.

Attajirin ya ke cewa abin da ya hada sa da Aliko Dangote shi ne kokarinsu na ganin sun yaki cututtuka a Duniya. Bill Gates ya ce ya na gaisawa da Dangote ya fahimci cewa su na da tarayya.

Mun fara kasuwanci ne a karshen shekarun 1970s. Bayan nan kuma duk mu ka kafa gidauniyoyi da nufin bunkasa kiwon lafiya da inganta ilmi wanda a yau duk Saharar Afrika babu irin Dangote.

Bayan tarayyar da su ka yi wurin harkar ilmi da inganta lafiya, Bill Gates yace shi da Dangote su na sha’awar shiga sana’a mai daukar idanu kamar siminti, takin zamani, gishiri da dai sauransu.

KU KARANTA: Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2020 na Tiriliyan 10 a Najeriya

Gates yake cewa ganawar nan da ya fara yi da Dangote a wajen taron na Birnin New York ya yi sanadiyyar Abokantarsu har gobe. A dalilin haka ne Bill Gates ya warewa Najeriya kudi Dala miliyan 100.

Mai kudin ya ware wannan makudan dalilin kudi ne a shekarar 2016 domin yaki da matsalar yunwa a kasar. Matsalar rashin abinci mai lafiya ne sanadin kusan rabin mutuwa 5 da ake yi a Najeriya.

Ba’Amurken ya nuna cewa ya fahimci babban hanyar kiwon lafiya shi ne ta samun abinci mai gina jiki. Haka zalika ya ce Amininsa Dangote ya fahimci wannan dabara kuma yake kokari a kasarsa.

Mista Gates wanda ya shafe shekaru kusan 20 ya na cikin sahun Attajiran Duniya ya karkare bayanin da ya yi shafinsa na GatesNotes.com da cewa shi da Maidakinsa Melinda su na tinkaho da Dangote.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel