Kotu ta girgiza Kana wa, ta ce babu hannun Gawuna da Murtala Garo a yaga sakamakon zaben mazabar Gama

Kotu ta girgiza Kana wa, ta ce babu hannun Gawuna da Murtala Garo a yaga sakamakon zaben mazabar Gama

Sabanin abin da jama'a suka sanu kuma suka gaskata a kan sakamakon zaben gama, Jastis Halima Shamaki, babbar alkaliyar kotun sauraron korafin zaben gwamna a jihar Kano, ta fadi abin da ya girgiza Kana wa a kan yaga sakamakon zaben.

Da tsakar dare ranar 10 ga watan Maris ne jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano suka kama mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, bayan an zarge su da yaga sakamakon zabe mazabar Gama a cibiyar tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Nasarawa.

Kafafen yada labarai sun rawaito cewa Gawuna da Garo sun dira cibiyar tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da ke kan titin zuwa filin jirgin sama tare da yayyaga sakamakon zaben mazabar Gama.

Amma, da take yanke hukunci a ranar Laraba, Jastis Shamaki, ta bayyana cewa Umar Tanko Yakasai, wakilin jam'iyyar PDP, shine wanda ya yaga sakamakon zaben mazabar Gama.

A hukuncin da ta karanta, Jastis Shamaki ta zargi Mista Tanko Yakasai da kulle kansa a cikin daki domin samun damar sauya sakamakon zaben.

DUBA WANNAN: EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara, sunaye da hotunansu

Abin da Jastis Shamaki ta fada ya wanke Gawuna da Sulen-Garo daga zargin da ake yi musu na yaga sakamakon zaben mazabar Gama, lamarin da yasa har jami'an 'yan sanda suka kama su a daren ranar 10 ga watan Maris.

"Takardun sakamakon zaben da masu korafi suka gabatar basu da hatimin hukuma, kuma babu saka hannu. Wasu kuma an yi rubutu a jikinsu, a saboda haka batun yaga sakamakon zabe ya zama jita-jita da kotu ba zata karba ba.

"Dakta Yakasai ya samu damar sauya sakamakon zaben da aka sace bayan ya rufe kansa a dakin da sakamakon zabe yake," a cewar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel