Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

- Wani jarumi mai suna Usman Yusuf Abubakar ya bige masu garkuwa da mutane har da sakin wadanda mutanen suka sace

- Daya daga cikin wadanda ya kubutar din ne ya bayyana yadda Usman ya kwace bindigar wanda aka baiwa tsaronsu

- Daga baya an samu labarin mutuwar wanda ya bige din har lahira bayan da 'yan uwansa ke bukatar cafkar jarumin

Wani jarumin mai abin hawa, Usman Yusuf-Abubakar, an ruwaito cewa ya buge masu garkuwa da mutane inda ya samu nasara tseratar da mutane masu yawa.

Daya daga cikin wadanda suka tsira, yace Yusuf Abubakar ya yi gumurzu da mai garkuwa da mutane ind aya yi nasara kwace makaminsa.

kamar yadda mutumin ya sanar kuma jaridar daily Nigerian ta ruwaito, bayan Yusuf Abubakar ya saki mutanen da masu garkuwa da mutane suka kama, ya kwashe makamansu inda ya yi cikin daji dasu.

KU KARANTA: Ke duniya: Matar uba ta kona 'yar kishiya akan 'rashin biyayya'

Wanda aka sakan ya ce, "An tsaremu tare da mana fashi. daga baya kuma aka yi garkuwa da mu. An jagorancemu zuwa ga wani mai garkuwa da mutane rike da bindiga kirar AK47 inda sauran 'yan uwansan suka tsaya don kwashe dukiyoyinmu,"

Ya kara da cewa, "A motata kadai, sun samu naira dubu dari hudu, wayoyi, laptop da sauransu. Muna kan hanyar shiga dajin ne usman ya bayyana inda ya sakemu tare da kwace makaman masu garkuwa da mutanen,"

"Ya bar mai garkuwa da mutanen a kassa kwance bayan da yai masa duka da raunika masu yawa. Daga baya mun samu labarin mutuwarsa daga bakin 'yan uwansa yayin da ake cinikin kudin fansar wani fasto."in ji shi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel