Tirkashi: Tun kafin kotu ta yanke hukunci Rarara ya fara yiwa 'yan Kwankwasiyya shagube
- A yayin da ake can ana yanke hukunci akan sakamakon zabe na gwamnan jihar Kano
- An nuno fitaccen mawakin nan na siyasa wato Rarara yana yiwa 'yan Kwankwasiyya shagube
- Mawakin ya ce tabbas Ganduje ne ya lashe zabe, saboda haka kotu kamar ta bayyana sunansa ne a matsayin wanda ya ci zabe
A yau Laraba 2 ga watan Satumbar shekarar 2019 ne kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano za ta yanke hukunci akan wanda yayi nasara a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a watannin baya da suka gabata.
A yayin da ake can cikin kotu alkalai na yanke shari'a tsakanin gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da abokin hamayyar sa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.
Yanzu haka dai an hasko fitaccen mawakin nan na siyasa na jihar Kano, wato Dauda Kahutu Rara wanda aka fi sani da Rarara, yana yiwa 'yan jam'iyyar PDP ma'ana 'yan Kwankwasiyya shagube.
KU KARANTA: Fitattun jarumai mata guda 9 da suka shahara sanadiyyar Adam Zango, jarumin yayi alkawarin karrama daya daga cikinsu
Ga dai abinda mawakin yake cewa a lokacin da wani dan jarida yayi masa wata tambaya dangane da sakamakon zaben sai ya ce:
"Kun manta cewa babu wani sarki bayan Allah? Wannan abu ya riga ya tabbata a kansu kamar yadda suka fada, sunce saura kwana uku, a karshe sun zo sun shiga uku, sun ce baza a rantsar ba, a karshe an zo an rantsar suna gani, haka a kotun ma duk wasu hujjoji sun tabbata cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine ya ci zabe.
"Kuma mu mun riga mun fidda sako ma, wanda muke cewa 'A kotun ma Ganduje ne, INEC ma Ganduje ne, murna Baban Abba ya ci a kotun ma an bayyana.'"
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng