Tazarcen Buhari a 2023: Buhari zai yi amai ya lashe kayansa - Buba Galadima

Tazarcen Buhari a 2023: Buhari zai yi amai ya lashe kayansa - Buba Galadima

A yayin da wasu bangarori a kasar ke kiraye-kirayen shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi ci gaba da mulkin kasar nan a wani sabon wa'adi na uku, mashahurin dan hamayya, Buba Galadima, yayi martani game da bukatar.

A fari dai wasu kungiyoyi da ke goyon bayan shugaba Buhari, sun nemi a yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima domin bai washugaban dama ci gaba da mulkar kasar na a wani sabon zango na uku.

Sai dai a wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ta barrantar da kanta daga kiraye-kirayen kungiyar da cewar ko kadan shugaba Buhari ba ya da sha'awar neman mulki a zango na uku.

Sanadiyar wannan lamari ya sanya jagoran kungiyar 'yan awaren jam'iyyar APC wato Buba Galadima, ya ce ko kadan bai gamsu da musantawar da gwamnati tayi ba domin ta dabi'antu da yin amai ta lashe kayanta a lokuta da dama da suka gabata kan wasu muhimman ababe da suka shafi kasa.

Hakazalika Buba Galadima ya ce tuni ya dawo daga rakiyar amincewa da gaskiya ko kuma adalcin kotukan kasar nan, duba da yanayin hukunce-hukuncen da suke yankewa kan kararrakin da suka shafi zabe.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi watsi da rade-radin da ke yaduwa na zargin zaman doya da manja da ke tsakanin sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, lamarin da ya ce kanzon kurege ne da shaci fadi da ke kai komo musamman a zaurukan sada zumunta.

KARANTA KUMA: An ceto bayi 23 daga kasar Burkina Faso zuwa Katsina

Farfesa Osinbajo yayin kawar da shakku da yi wa 'yan adawa raddi, ya ce babu abin da ke tsakanin sa da shugaban kasa Buhari face biyayya sau da kafa da kuma yi wa juna kyakkyawan fata nagari.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, wannan sako na kunshe ne cikin wata mujalla mai sunan "This is Nigeria" wato "Wannan ce Najeriya" da aka rarraba yayin murnar zagoyar ranar samun 'yancin kan Najeriya a ranar Talata 1 ga watan Oktoba a wata liyafar dare da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a birnin Abuja.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel