Wasu yan iska sun kashe wata mata da yarta a Kano
Wasu yan iska sun kashe wata mata da yarta a kwatas din Gobirawa Yan Yashi, wani unguwar talakawa da ke karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Yan sanda a jihar sunce lamarin ya afku ne a ranar Lahadi da tsakanin karfe 8 da 9 na dare, Sannan cewa an rigada an kama mutane shida da ke da hannu a laifin.
Kakakin yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da kamun, yace kwamishinan yan sandan jihar, Mista Ahmed Illiyasu, ya jagoranci jami’an Operation Puff-Adder wajen kama masu laifin.
Yace an kwato muggan makaman da aka yi amfani da su wajen kaddamar da harin.
An tattaro cewa mijin matar, Malam Sha’aibu Abdulmumin ya tafi biki lokacin da abun ya afku.
Yan sandan sunce an fara bincike a lamarin sannan cewa da zaran an gama za a mika su kotu.
KU KARANTA KUMA: Yadda fitaccen dan kwallon kafa Sadio Mane ya ginawa Musulmai Makaranta, Masallaci da Asibiti a kasar Senegal
A wani labarin kuma mun ji cewa jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) a Kano sun cafke shugaban hukumar CRC (Committee Reorientation Council Chairman) a karamar hukumar Madobi, Alhaji Sanusi Yola, mataimakinsa, Abdulkarim K. Jubril, da shugaban jam'iyyar APC na yankin, Surajo Usman Kubarachi, bisa zarginsu da tafka badakala a cikin shirin ciyar da dalibai kyauta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wata majiya mai kwari a cikin hukumar DSS ta sanar da ita cewa mutanen uku na amsa tambayoyi bisa zarginsu da cutar mutanen da aka dauka aikin girka abincin da za a bawa daliban firamare a yankin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng