Mutuwa rigar kowa: Suna murnar sayen sabon injin janareto, ashe basu san cewa shine zai zama ajalinsu ba

Mutuwa rigar kowa: Suna murnar sayen sabon injin janareto, ashe basu san cewa shine zai zama ajalinsu ba

- Wani mummuman lamari da ya faru a wani kauye dake cikin jihar Imo ya bar mutane cikin jimami

- Yayin da suka wayi gari suka tarar da injin janareto ya kashe wani mutumi matarsa da kuma 'yarsu guda daya

- Wannan lamari ya tada hankalin mutanen kauyen inda suka yi cirko-cirko suna jimamin wannan lamarin

Wani mummunan abu da ya faru a jihar Imo a safiyar ranar Litinin dinnan da ta gabata shine yadda injin janareto ya kashe dangi guda gaba daya.

Lamarin ya faru a kauyen Umuoparaemeka dake cikin karamar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo.

Wannan kauye dai sun tashi da wannan jimami ne a safiyar ranar Litinin din, yayin da wani mutumi mai suna Lucius Iwunze, da matarshi Ngozi da kuma 'yarsu guda daya mai suna Geraldine suka mutu duka bayan sun shaki hayakin injin janareton.

Wani dan kauyen ya bayyana cewa 'yan uwan mamatan sun zo gidan da safiyar ranar sai suka tara da kofar a kulle ne daga ciki.

KU KARANTA: Innalillahi: 'Yan sanda sun ceto mata 19 da tsohon ciki a wani gida da ake dirka musu ciki idan sun haihu a sayar da jariran

Ya cigaba da cewa, sai suka yi ta kwankwasawa amma shiru babu wanda ya bude, hakan ya sa suka kira makwabta aka taru aka bude kofar gidan da karfin tsiya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Imo, Orlando Ikokwu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka jami'ansu sun fara gabatar da bincike akan lamarin, inda ya kara da cewa DPO na yankin ya kai shi wajen da lamarin ya faru inda suka tarar da gawarwakin mutane ukun a cikin gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel