Yancin kai: Sheikh Ahmed Gumi ya yi jawabi na musamman

Yancin kai: Sheikh Ahmed Gumi ya yi jawabi na musamman

Shahararren malamin nan na Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, yace mizanin da Najeriya ta taka a shekara 59 yana da matukar birgewa sannan cewa nasarar da aka samu ba laifi.

Gumi, wanda aka haifa a ranar da Najeriya ta samu yanci, yace: “babban abun farin ciki ne gare ni yadda ranar haihuwana ya kama ranar samun yancin kanmu... duba ga yadda abubuwa suke faruwa a kasar sannan a matsayina na mutum, mizanin ba laifi kuma akwai nasara sannan mun gode Allah.

“A shekara 59, ina ganin Najeriya na akan mataki na 3, sannan akwai baban aiki a gaba da sadaukarwa domin samun nasara mai kyau. Bamu gama fita daga kalubale ba, amma babu shakka akwai haske anan gaba sosai. Ina da yakinin cewa muna fuskantar abune da ba zamu iya gujewa ba a matsayin karamar matashiyar kasa mai jama’a daban-daban.”

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka

A wani lamarin kuma,mun ji cewa tsohon mai ba shugaban kasa Shehu Shahttps://facebook.com/legitnghausagari shawara kan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa shekaru 59 bayan samun yancin kai, Najeriya bata kai inda magabatanta suke sanya ran zata kai ba ta fannin cigaba.

Da yake hira da jaridar Daily Trust a jiya Litinin, 30 ga watan Satumba, Yakasai yace koda dai Najeriya ta samu wasu cigaba, abunda ake ya tsammani shine cewa kasar zata zarra sosai fiye da yadda take a yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel