NDLEA: Mutane fiye da 250, 000 sun yi cincirindo kan aikin mutum 5000
NDLEA mai yaki da safara da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta bayyana cewa akalla mutum 250, 000 ne su ka nuna sha’awarsu na samun aiki bayan tallata shirin daukar ma’aikata.
Hukumar ta ke cewa sama da mutum 250, 000 sun cike sunayensu a shafin neman daukar aiki inda ake bukatar mutanen da ba su wuce 5, 000 ba. Hakan na nufin kashi 2% rak ne za su dace da aikin.
A cewar hukumar, ba ta kai ga fara tantanace wadanda za a dauka aikin ba tukuna. A Ranar 29 ga Watan Agustan 2019 ne aka rufe shafin da aka kafa domin daukar masu sha’awar aiki a hukumar NDLEA.
Hukumar yaki da shan kwayoyi na kasar ta kara wa’adin mako guda domin wadanda ba su karasa cike sunayensu da abubuwan da ake bukata a shafin daukar aikin ba saboda wasu dalilai su karasa.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar ta NDLEA, Jonah Achema, ya yi watsi da rade-radin da ke yawo inda tabbatar cewa ba a kai ga fara gayyatar wadanda za a dauka aikin ba tukuna.
KU KARANTA: Gwamnan Adamawa ya yi wa wasu 'yan gidan yari afuwa
Jonah Achema ya bayyana wannan ne lokacin da ya zanta da Manema labarai a Abuja. Acehma yake cewa ba su kira kowa da nufin a tantance wadanda za a ba aikin na yaki da miyagun kwayoyi.
“Za a tuntubi wadanda su ke neman aikin kuma su ka dace a lokacin da ya dace. Masu neman aikin sun yi watsi da duk wani labari da ke yawo da ba daga hukumar ya fito ba a matsayin jita-jita.”
Idan ba ku manta ba kwanaki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni a dauki sababbin ma’aikata 5000 a hukumar NDLEA domin ganin an yaki mummunar dabi’ar shan kwayoyi.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng