'Yancin kai: Mun ba Iyayen gidanmu kunya - Tsohon 'Dan siyasar Arewa

'Yancin kai: Mun ba Iyayen gidanmu kunya - Tsohon 'Dan siyasar Arewa

Wani tsohon mai ba shugaban kasa Shehu Shagari shawara kan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa shekaru 59 bayan samun yancin kai, Najeriya bata kai inda magabatanta suke sanya ran zata kai ba ta fannin cigaba.

Da yake hira da jaridar Daily Trust a jiya Litinin, 30 ga watan Satumba, Yakasai yace koda dai Najeriya ta samu wasu cigaba, abunda ake ya tsammani shine cewa kasar zata zarra sosai fiye da yadda take a yau.

“Idan Za mu kwatanta kanmu da sauran kasashe irin su Indiya, Brazil da Malaysia, Za mu gano cewa sun yi mana nisa sosai sannan wannan ba shine abunda magabatanmu suka so ba,” inji shi.

Tsohon dan siyasan yace domin samun cigaba, ya zama dole yan Najeriya su Gina damokradiyya sannan su jajirce wajen bin umurninta.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa: NEMA ta gargadi mazauna wasu garuruwa 4 da su yi gaggawan tashi

“Halayyar wasu shugabannin Najeriya na rusa damokradiyyarmu. Muna kiran kanmu kasar damokradiyya amma a gaske mun san cewa ba haka muke ba saboda kasar damokradiyya, shugabannin jam’iyyu ne akan abubuwa ba wai mutum guda ba. Koda a wajen da kaga mutum guda ke jan ragamar abubuwa, yan jam’iyyar ne suka zabi cewa mutum guda yayi jagoranci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel