EFCC ta sake gurfana da wani sanatan Najeriya kan zambar N3.1bn

EFCC ta sake gurfana da wani sanatan Najeriya kan zambar N3.1bn

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, ta sake gufanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, akan wasu tuhume-tuhume guda tara da suka hada da zambar kudi a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

An sake gufana da Mista Suswam, wanda ya kasance sanata mai ci a gaban Justis Okon Abang tare da Omadachi Oklobia wanda ya kasance kwamishinan kudi a Benue lokacin da yake matsayin gwamna.

Su dukka biyun sun ki amsa laifi akan dukkanin tuhume-tuhume da ake masu sannan an bayar da belinsu bisa ga ka’idojin da Justis Ahmed Mohammed ya basu a baya bayan an gurfanar da a gabansa a shekarar 2015.

Justis Abang a bukaci lauyan da ke cikin lamairin da ya ba kotu hadin kai inda yayi gargadin cewa ba zai lamunci duk wani bukata na neman dage shai’an ba.

Mista Abang ne ya cigaba da shari’an Mista Suswam, biyo bayan janyewa da Justis Mohammed yayi daga shari’an.

KU KARANTA KUMA: An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukuncin a shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto

Mista Mohammed ya yi nun ga wani labara da Sahara Repoters ta wallafa inda ta zarge shi da kokarin yiwa Mista Suswam sassauci a matsayin dalilinsa na janyewa daga shari’an.

A yanzu an dage sauraron shari’an zuwa ranakun 29, 30 da kuma 31 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng