Maina: Kotu ta tursasawa Abubakar Malami ya wallafa kadarorin da ya karbe

Maina: Kotu ta tursasawa Abubakar Malami ya wallafa kadarorin da ya karbe

Babban kotun tarayya da ke zama a Legas ta yanke hukunci game da shari’ar da ake yi tsakanin wani Lauya da kuma gwamnatin Najeriya game da binciken AbdulRasheed Maina da ake yi.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Guardian a yau Litinin, 20 ga Watan Satumbam 2019, Alkali ya nemi a fito da sunayen duk kadarorin da aka karbe daga hannun AbdulRasheed Maina.

Kotu ta umarci Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa su bi wannan umarni.

Alkali mai shari’a Oluremi Oguntoyinbo ta ce gwamnati ta wallafa jerin duk wasu kadarori da dukiyoyin Alhaji Maina da aka karbe a Najeriya a binciken da ake yi babban tsohon jami’in kasar.

Wata kungiya ce mai zaman kan ta, ta nemi kotu ta umarci gwamnatin tarayya ta hannun ofishin babban Lauyan gwamnati AGF da EFCC su bayyana kadarorin da aka karbe a wajen Alhaji Maina.

KU KARANTA: CAN ta gana da Osinbajo kan zargin karbar biliyoyi na zaben 2019

Alkali ya gamsu da wannan kara da kungiyar “Centre for Law and Civil Culture” ta shigar inda ya amince da rokon na ta na cewa ya kamata Duniya ta san abin da aka karbe daga hannun Alhaji Maina.

Bayan nan kuma Oguntoyinbo ta yi na’am da karin lokacin da kungiyar ta ke bukata a karar da ta shigar mai lamba ta FHC/L/CS/756/2019 da Ministan shari’ar Najeriya a madadin gwamnatin kasar.

AbdulRasheed Maina ya rike kwamiti ne da ya yi aiki a kan harkar fansho a Najeriya inda aka zargesa da wawurar makudan miliyoyin kudin tsofaffin ma’aikata wanda har yau ake faman tirka-tirka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel