Shugaba Buhari ya yi furuci a kan bankado wani gida da aka daure kananan yara 300 a Kaduna
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Alla-wadai da cin zarafin kananan yara a wani gida da jami'an 'yan sanda suka bankado a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna.
A wani jawaba da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Asabar a Abuja, shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da duk wani nau'in cin zarafin mutane, manya da kanana, ko take musu 'yanci.
Buhari ya yaba wa rundunar 'yan sanda bisa daukan matakan gagga wa bayan sun gano gidan. Kazalika, ya ce dole a bawa yara kariya daga duk wasu masu mugun nufi.
Wani bangare na jawabin ya ce: "gwamnatin shugaba Buhari ta yaba wa kokarin rundunar 'yan sanda na bankado wani gida a jihar Kaduna da ake cin zarafin kananan yara da sunan gidan horon kangararrun yara. Gwamnati na ba zata taba yarda da cin zalin mutane, manya ko kanana ba.
"Mun yi farin cikin cewa al'ummar Musulmi sun yi watsi da bayyana wurin a matsayin makarantar Islamiyya.
DUBA WANNAN: Hameed Ali ya zayyana dalilai biyu da suka sa FG ta rufe iyakokin Najeriya
"Wurin ya fi kama da inda ake azabtar da yara tare da bautar da su.
"Burin shugaban kasa shine ganin an bawa yara kariya daga barinsu suna gararamba a titi, inda daga nan ne suke fada wa hannun miyagun mutane.''
A ranar Alhamis ne Legit.ng ta wallafa cewa jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun bankado wani gida a cikin garin Kaduna da aka tara yara masu kananan shekaru da masu matsakaita shekaru, wasunsu kuma daure da mari.
Gidan talabijin na TVC ya rawaito an gano wannan gida ne a unguwar Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi, kuma daga cikinsu akwai kananan yara da basu wuce shekaru 10 ba, inda yaran suka tabbatar da cewa ana yin luwadi dasu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng