Arewa ta na bukatar jagora kamar Kwankwaso - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Arewa ta na bukatar jagora kamar Kwankwaso - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

- Shugaban majalisar malamai na kasa reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil yayi wani karin haske dangane da halin da arewa ke ciki

- Malamin yayi maganar ne akan irin cin mutunci da rashin girmama na gaba da mutanen yankin arewa suke yiwa shugabannin su

- Hakan ya sa Shehin Malamin ya ce yankin na arewa yana bukatar jagora jajirtacce irin tsohon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

An bayyana yanayin da yankin arewa ke ciki a yanzu a matsayin yanayı da yake bukatar jagorori da zasu yi magana a tsaya kuma a saurare su sannan ayi aiki da ita, kamar dai tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan bayanı dai ya fito daga bakin shugaban majalisar Malamai na reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, a wata zantawa da yayi da wakilan jaridar Leadershi a Kano.

Sheikh Khalil ya kara da cewa babban kalubalen da yankin arewa ke fama da shi a wannan lokacin shine rashin kwakkwaran jagora guda daya wanda zai jagoranci al'ummar yankin zuwa ga tudun mun tsira, sai dai kuma malamin yana alakanta wannan matsala da rashin girmama na gaba da shuwagabanni.

KU KARANTA: To fa wata sabuwa: Ga masu neman sanin dangantaka ta da Sadiya Haruna, to daga tau ku sani matata ce - Cewar Isa A Isa

Malamin ya ce, duk wani mutumi da aka dauko aka kawo a matsayin wanda zai jagoranci jama'ar yankin arewa, maimakon a dinga girmama shi, sai dai kaga an rufar masa da sara da suka na zagi da batanci. Sannan ya cigaba da cewa hatta mutumin da ya kawo sunan jagoran shi ma bai tsira ba a wannan zagin da kuma sharri na mutane. Sabanin abinda ke faruwa a yankin kudu maso yamma, wato yankin Yarabawa, mutanen da a kowanne lokaci suke yin biyayya sau da kafa ga manyan su, kuma suke bin alkibila guda daya tun daga kan Awolowo har zuwa kan Tinubu a wannan lokacin.

Kamar yadda jaridar ta Leadership Hausa ta ruwaito ta ce, Shehin Malamın ya bayyana, ya ce, yankin Arewa suma suna bukatar mutum jajirtacce irin Kwankwaso, mutum mai gaskiya da amana, wanda baya yaudara kuma yake da cikakken tsarin da zai dore.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel