To fa wata sabuwa: Ga masu neman sanin dangantaka ta da Sadiya Haruna, to daga tau ku sani matata ce - Cewar Isa A Isa

To fa wata sabuwa: Ga masu neman sanin dangantaka ta da Sadiya Haruna, to daga tau ku sani matata ce - Cewar Isa A Isa

- Jarumi Isa A. Isa yayi wata babbar magana a wani sabon bidiyo da ya wallafa

- Inda ya bayyanawa mutane masu yawan tambayarsa dangantakar dake tsakaninsa da Sadiya Haruna

- Jarumin ya bayyana cewa daga yau kowa ya sani cewa Sadiya Haruna matarsa ce

Wani bidiyo da jarumin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood yayi ya bayyana dangantakar dake tsakaninsa da Sadiya Haruna, buurwar da ta ware waken bayar da shawarwari akan zaman aure da yadda mace zata rike miji ba tare da samun matsala ba.

Jarumin dai ya bayyana cewa ana yawan tambayarshi dangantakar dake tsakanin shi da Sadiya Haruna, to yaş shine yayi alkawarin bayyanawa, ga abinde jarumin ya ce:

“Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta’ala Wabarakatuhum, jama’a kowa ya taso sai ya fara tambayata Isa wai yaya dangantakarshi tsakanin shi da Sadiya, kowa ba shi da aiki sai wannan, saboda haka daga yau ita matata, nagode.”

KU KARANTA: Tirkashi: Tsohuwa ‘yar shekara 87 ta kashe jikanta saboda tana ganin babu wanda zai kula dashi bayan ranta

Ana yawan ganin jarumin da Sadiya Haruna suna yawo tare ko kuma suna daukar hoto ko bidiyo tare.

Idan ba a manta ba Sadiya Haruna dai ita ce wacce jami’an ‘yan sanda suda kama ta kwanakin baya, bayan zargin ta da aka yi da yiwa casu manyan jaruman Kannywood kazafi akan abin basu ji ba basu kuma gani ba.

To amma kuma abinde jarumin ya fada ya bar wası mutane da yawl a cikin duhu, domin kuwa babu wanda yasan lokacin da suda yi aure, ko kuma wani wanda ya halarci daurin auren su, hakan ne ma ya sanya wasu mutane ke kalubalantar shi akan ya bayyana yadda aka yi ta zama matarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng