Tirkashi: Tsohuwa ‘yar shekara 87 ta kashe jikanta saboda tana ganin babu wanda zai kula dashi bayan ranta

Tirkashi: Tsohuwa ‘yar shekara 87 ta kashe jikanta saboda tana ganin babu wanda zai kula dashi bayan ranta

- Wata tsohuwa mai shekaru 87 ta dauki rayuwar wani karamin jikanta

- Tsohuwar ta bayyana chew tayi hakan ne saboda ta na tsoron halin da yaron zam shiga bayan ranta

- Yanzu haha dai jami’an hukumar ‘yan sandan garin sun kama ta sun tai da ita domin gabatar da bincike a kanta

Kamar yadda jaridar ABC ta ruwaito, wata tsohuwa mai shekaru 87 a duniya mai suna Lilian Parks ta bayyana dalilin da ya sanya ta kasha jikanta saboda tana ganin cefa babu wanda zai kula mata dashi bayan ranta.

A yadda rahoton ya bayyana, Joel, marigayin yana zuwa ya zauna da kakar tashi kowanne karshe sati, sannan a ranekun aiki kuma sai yaje zauna da delibai ‘yan uwanshi.

An gano gawarshi ne bayan ‘yar uwarshi taje ta duba shi a gidan kakarsu radar Lahadi dinnan da ta gabata.

Jami’an hukumar ‘Yan sanda na Bradenton sun kama tsohuwar inda suka wuce da ita domin yin gwaji a kwakwalwarta da kuma duba lafiyarta kafin a kaita kotu a yanke mata hukuncin kisa.

KU KARANTA: Babbar magana: Babu abinda na tsana a rayuwata fiye da namiji - In ji Huddah

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce:

“Wannan al’amari ne babba ga jami’an mu. Banu ji dadi ba kwata-kwata ace mutum yana tunanin daukar ran wani saboda yana ganin ceza idan babu shi ba zam somu kulawar da ta kamata ba.”

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Bradenton din, mahaifin Joel ya rasu, mahaifiyar shi kuma tabi nesa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel