Shamsiyya ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta saboda baya sallah

Shamsiyya ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta saboda baya sallah

Wata matar aure, Shamsiyya Dikko, a ranar Alhamis ta roki kotun shari’an Musulunci da ke zama a Rigasa, Kaduna da ta rushe aurenta da Aminu Umar, kan cewa baya son yin sallah.

Mai karar wacce ke zama a Rigasa, ta kuma roki kotu da ta raba aurensu kan hujjar cewa Umar ya kasance dan kwaya na kin karawa wanda ya gaza sauke hakkin iyalinsa.

“Tsawon watanni tara ina zama tare da iyayena saboda halin mijina. Bai taba ziyarta na ba koda sau guda domin ya bani hakuri akan hallayarsa,” kamar yadda ta fada ma kotu.

A nashi bangaren Umar ya karyata zarge-zargen da ake akansa cewa shi sigari kawai yake sha.

Umar ya fada ma kotu cewa har yanzu shi yana son matarsa.

Ya bayyana cewa yayi duk kokarinsa don ganin ya magance matsalolin sannan cewa ya hadu da surukansa bayan matar ta bar gdansa domin ta koma dakinta amma ta ki.

Ya roki kotu da ta kara masa lokaci domin ya sasanta da matarsa.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya haikewa abokiyar aikinsa har lahira, ya kuma boye gawar ta

Bayan sauraron bangarorin biyu, alkalin, Malam Dahiru Bamalli, ya umurci ma’auratan da su sasanta kansu domin tsratar da aurensu.

Bamalli ya umurce su da su gabatar da iyayensu ko wakilansu a kotu idan sasancin bai yiwu ba. Ya dage zaman har zuwa ranar 18 ga watan Disamba, domin sasanci ko raba auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel