To fah: 'Yan Kudu sunyo caa akan Hausawa yayin da aka kama 'yan damfara guda 6 Hausawa a jihar Kano

To fah: 'Yan Kudu sunyo caa akan Hausawa yayin da aka kama 'yan damfara guda 6 Hausawa a jihar Kano

- Ana ta samun kace nace a shafin sadarwa na Twitter, inda 'yan Najeriya mazauna kudancin kasar suka yo caa akan 'yan arewa

- 'Yan Kudun sun fara maganganu ne akan 'yan arewan bayan kama wasu Hausawa da hukumar EFCC ta yi a jihar Kano suna damfara a yanar gizo

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawan ta jihar Kano ta kai sumamen kama wadanda take zargin ne a unguwar Hotoro dake jihar Kano bayan samun bayanan sirri akan su

'Yan Najeriya musamman 'yan kudancin kasar sun yi caa akan 'yan yankin arewa bayan kama wasu 'yan damfarar yanar gizo (Yahoo Boys) da aka yi guda shida a jihar Kano.

Rundunar hukumar yaki da cin hanci da rashawa reshen jihar Kano ita ce tayi wannan kamu a ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar nan, inda suka kai sumame gidan da 'yan damfarar suke a gida mai lamba 282 dake unguwar Hotoro cikin jihar ta Kano.

Rundunar jami'an EFCC din sun kai sumamen ne bayan bayanin sirri da suka samu akan mutanen da ake zargin. Mutanen da aka kama din sun hada da Bala Balarabe, Abdullahi Musa, Abdullahi Danladi, Bashir Kassim, Saleh Mustapha da kuma Abubakar Ahmed.

KU KARANTA: Wasu gawarwaki sun ga ta kansu yayin da aka kwakwalo su daga kabari wata daya da binne su akan rabon gado

An kama mutanen da wayoyi na zamani guda goma sha daya da kuma mota kirar Mercedez C300, yanzu haka dai za a gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu bayan an kammala bincike a kansu.

Wannan kamawar da aka yiwa 'yan damfarar wadanda suke duk Hausawa ne yasa mutane 'yan yankin Kudu suka yo caa akan 'yan arewa bayan kurarin da suka yi a kwanakin baya na cewa ba a taba kama dan damfara na yanar gizo Bahaushe ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng