Izala ta yi Allah wadai da cin fuskar da yan Kwankwasiyya suka yi ma Pantami

Izala ta yi Allah wadai da cin fuskar da yan Kwankwasiyya suka yi ma Pantami

Kungiyar addinin musulunci ta Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah dake Najeriya ta yi tir, tare da Allah wadai bisa ihun cin mutunci da cin fuska da yayan kungiyar darikar siyasar Kwankwasiyya suka yi ma Malam Isah Ali Pantami.

Izala ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa data fitar a shafinta na yanar gizo https://www.jibwisnigeria.org inda ta nuna bacin ranta ga abinda magoya bayan Sanata Rabiu Kwankwaso suka yi ma Ministan sadarwar Najeriya, Isah Ali Pantami

KU KARANTA: Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi

Legit.ng ta ruwaito wani bidiyo da a yanzu haka ya karade kafafen shafukan sadarwar zamani na dauke da yadda wasu daga cikin mabiya darikar siyasar Kwankwasiyya suka ci mutuncin fitaccen Malamin addinin Islama kuma Ministan a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin wannan bidiyon ana iya ganin Sheikh Isah Ali Pantami, jami’an tsaro da kuma yaran Kwankwasiyya, inda yan Kwankwasiyyan suke yi ma Sheikh Pantami ihun ‘Ba ma yi’, wasu ma suna kokarin cafko shi yayin da jami’an tsaro suka yi ta kokarin kareshi.

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Talata, 24 ga watan Satumba a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano dake garin Kano a daidai lokacin da Ministan yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Kano, su kuma yan Kwankwasiyya zasu tafi Legas.

Hakan ne tasa shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau yace: “wannan al'amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al'qur'ani, masanin tafsiri, wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu 'yan Siyasa zasu masa irin wannan cin mutunci tabbas an aikata laifi Babba.

“Ya kamata jagoran kwankwasiyya Dakta Rabi'u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa yan uwa musulmi da shi kansa Dr. Isa Ali Pantami hakuri, sa’annan yamja kunnen mabiyansa, domin duk wanda zai taba Malami ya saurari fushin Allah, Domin Annabi SAW Yace Malamai magada Annabawa ne.” Inji shi.

Daga karshe Malamin yace Annabi yace girmama malamai mahaddata Al-Qurani na daga girmama Allah, sa’annan kuma hakan ya saba wa tsarin mulki kasa domin Malamin yana rike da mukami a majalisar zartarwa ta Nigeria, hakan ka iya zama cin mutunci ga ita kanta gwamnati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel