Gwamna Zulum ya bawa matashin da ya lashe gasar Alqur'ani kyautar N5m, sabuwar mota da sauransu
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bawa matashin nan, Idris Abukakar Muhammad, kyautar makudan kudi, miliyan N5, tare da gaureriyar sabuwar mota kirar Toyota Corolla biyo bayan nasarar da ya samu a gasar musabaqar Alqur'ani ta kasa da kasa.
Bayan kyautar kudi da mota, gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun matashin har zuwa matakin digiri na uku tare da alkawarin bashi aiki kyauta bayan ya kammala karatunsa.
Matashin mai shekaru 20, mazaunin sansanin 'yan gudun hijira (IDP) a Maiduguri, ya zama zakara a gasar musabaqar Alqur'ani da aka gudanar a kasar Saudiyya kwanan nan.
DUBA WANNAN: Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli
Goni Adam Muhammad, kawu a wurin matashin, shine ya kawo shi sansanin 'yan gudun hijira daga karamar hukumar Marte kafin ya kammala haddar Alqur'ani.
Wani ma'aikacin gidan rediyo da talabijin na jihar Borno (BRTV), Abdulsalam Mohammed, wanda ya halarci gasar musabaqar da aka yi a birnin Makkah, ya shaidawa Daily Trust cewar nasarar matashin, nasara ce ga jihar Borno da Najeriya baki daya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng