An sake kama wani dan Najeriya kan safarar miyagun kwayoyi a Indiya

An sake kama wani dan Najeriya kan safarar miyagun kwayoyi a Indiya

An kama wani dan Najeriya mai suna Samson Maxwell, bayan an same shi dauke da damin hodar iblis a Pune, wani birni a kudancin Indiya da ke Maharashtra.

Wani rahoto da Hindustantimes, jaridar kasar Indiya ta wallafa a ranar Litinin tace an samu Mista Maxwell dauke da hodar iblis mai nauyin gram 32.20 wanda ya kai kimanin naira miliyan 1.5.

Jami’an yan sandan Pune sun bayyana a wani jawabi cewa kamun nashi ya biyo bayan wani bayanan kwararru da aka samu daga jami’an kwastam a lokacin manatee da aka kai gidan Mista Maxwell a Undri, Maharashtra.

A cewar rahoton, kamun Mista Maxwell ya biyo bayan kamun wani dan Najeriya, Uba Godwin mai shekara 31 akan samunsa da hodar iblis mai nauyin gram 200.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kone yaro Musulmi dan shekara 15 a Indiya saboda yaki komawa addinin Hindu

An kama Mista Godwill ne a kusa da wani wajen gidaje a Kondhwa lokacin da ya je wajen don siyar da hodar iblis.

Kwamishinan kwastam na Pune, Vishali Patange, a Wani jawabi yace Maxwell ya yarda cewar yana dauke da miyagun kwayoyin wanda na siyarwa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel