Dandalin Kannywood: Hafsat Idris tayi bikin samun mabiya miliyan daya a shafin Instagram

Dandalin Kannywood: Hafsat Idris tayi bikin samun mabiya miliyan daya a shafin Instagram

Shahariarriyar jarumar nan ta Kannywood, Hafsat Idris, tayi bikin samun magoya baya miliyan daya a dandalin sadarwa ta Instagram.

Da take sanar da farin cikinta akan haka, jaruma Hafsat, wacce aka fi sani da Hafsat Barauniya sakamakon rawar ganin da ta taka a fim din barauniya ta wallafa hotuna da bidiyon ta inda take godiya ga mabiyanta da abokan aikinta akan wannan sabon mataki da ta hau na mallakar mabiya miliyan daya.

Ta rubuta cewa “magoya baya miliyan daya, ina godiya a gare ku.”

Domin taya ta murna, manyan jaruman Kannywood, daraktoci da furodusa sun taya ta murna sannan suka yi mata fatan alkhairi.

Wasu daga cikin manyan fitattun Kannywood da suka taya murna sun hada da, Ali Nuhu, darakta Kamal S Alkali, Fati KK, Uzee Usman, Maryam Booth da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Ta leko ta koma: Kotun zabe ta tsige yan majalisa 2 na APC, tayi umurnin maye gurbinsu da yan PDP

Jarumar wacce ta kasance haifarfiyar garin Shagamu ta kasance shugabar kamfanin Ramlat Investment, wacce a kwanan nan ta sak wani babban fim da yayi fice a 2019 mai suna ‘Kawaye’, fim din da ya kunshi manyan Jarumai kamar su Ali Nuhu, Sani Danja, ita kanta da kuma kawarta Aishatu Humaira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng