Hukumar NDLEA ta kama dilolin kayan maye a hedikwatar jam'iyyar APC a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama dilolin kayan maye a hedikwatar jam'iyyar APC a Jigawa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa ta ce ta kama diloli tare da masu amfani da kayan maye 16 a cikin garin Dutse, babban burnin jihar Jigawa.

Mataimakin shugaban hukumar a jihar Jigawa, Mista Oko Michael, ya tabbatar da kama mutanen ga manema labarai.

Ya ce an kama masu laifin ne a harabar hedikwatar jam'iyyar APC da ke cikin garin Dutse.

Mista Oko ya bayyana cewa jami'an hukumar NDLEA sun kai samame wurin ne ranar Lahadi bayan samun korafi daga jama'a a kan yadda batagari suka mayar da wurin cibiyar sha tare da hada-hadar kayen maye a wurin.

DUBA WANNAN: Kudin yakin neman zabe: Shekarau, Wali da Mansur sun shiga 'tsaka mai wuya'

"Mun kai samame wurin ne bayan mun samu korafi da dama daga wurin jama'a a kan yadda wasu batagari suka mayar da harabar hedikwatar jam'iyyar APC da ke Dutse, babban birnin jiha, ciyar sha da fataucin kayen maye," a cewarsa.

Ya bayyana cewa an samu kullin tabar wiwi yayin da aka kama matasan tare da bayyana cewa za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binncike.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC a jihar Jigawa, Alahji Nasiru Dahiru, ya tabbatar da kai samamen da jam'an hukumar NDLEA suka yi, amma ya musanta cewa masu laifin mambobin jam'iyyar APC ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel