Limami ya shiga wasan buya, yayin da aka kama shi ya yiwa yarinya 'yar shekara 12 ciki

Limami ya shiga wasan buya, yayin da aka kama shi ya yiwa yarinya 'yar shekara 12 ciki

- Wani limamin coci ya dirka wa yarinya yar shekara 12 ciki a jihar Edo

- Tun bayan afkuwar lamarin dai saii Faston ya shiga wasan buya inda aka neme shi aka rasa

- An tattaro cewa faston kan kebe da yarinyar wacce a yanzu aka nema aka rasa idan an kammala ayyukan bauta

Rahotanni sun kawo cewa wani limamin coci ya tsere inda ya shiga wasan buya, bayan yayi ma yarinya yar shekara 12 fyade a jihar Edo.

Limamin cocin mai suna Pastor Marvelous Odalo Eranto-Eranto na fuskantar suka bayan an zarge shi da yin lalata da kuma dirka ma wata yarinya yar shekara 12 ciki.

A cewar wani jawabi daga Harrison Gwamnishu jagoran shirin Behind Bar Initiative (BBI), ya bayyana cewa yar’uwar faston ta kai yarinyar asibiti don zubda cikin. An kuma tattaro cewa tun bayan da ta tafi da ita ba a sake ganinta ba tsawon kwanaki hudu.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Yadda wani tsuntsu ya juye ya koma wata mata tsohuwa tukuf a jihar Legas

Faston yana lalata da ita ne a cikin sirri bayan an kammala ayyukan bauta a cocin.

Iyayen wacce lamarin ya fatu da ita sun kasance cikin bakin ciki bisa rashin ganin yarinyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel