An gano gawar kwamanda a rundunar soji a cikin wata rijiya da ke barikin sojoji a Kaduna

An gano gawar kwamanda a rundunar soji a cikin wata rijiya da ke barikin sojoji a Kaduna

An gano gawar O.O Ogunada, kwamanda a rundunar sojojin ruwa (Navy), a cikin wata rijiya maras zurfi da ke daf da wata Cocin 'Deeper Life' a cikin barikin sojoji ta 'Jaji' da ke jihar Kaduna.

An bayyana bacewar marigayiyar, mazauniyar Jaji, a ranar Juma'a, 12 ga watan Satumba, tare da tabbatar da bacewar ta bayan ba a ganta a wurin aiki ba ranar Litinin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa majiyarta a cikin barikin sojoji da ke Jaji ta sanar da ita cewa an jibge gawar babbar sojar a cikin rijiyar ne bayan an kashe ta.

Wasu majiya a barkin soji da ke Jaji da basu yarda a ambaci sunansu ba sun bayyana cewa, "an yi kokarin a same ta a waya bayan ba a ganta ba, amma daga baya sai aka gano cewa wayarta ta hannu da take shiga na cikin gidanta da ke rufe a cikin barikin.

"Ragowar lambobin wayarta basa shiga, lamarin da yasa aka balle kofar gidanta aka shiga domin a dauko wayarta da ake samu, wacce kuma ta bari a cikin gidan.

"An ga alamun zubar da jini a kan zanin gadonta da tufafinta da dakinta na kwanciya har zuwa bandaki da kuma wurin ajiye motar ta, inda aka gano motar ta bata nan."

DUBA WANNAN: Matatun man fetur 3 da zasu fara tace mai a mulkin Buhari - NNPC

Daily Trust ta rawaito cewa rundunar soji ta saka ido a kan masu yi mata aiki da 'yan uwanta, lamarin da ya kai ga an cafke wasu mutane biyu yayin da suke kokarin sayar da motar ta a garin Zariya.

Majiyar jaridar ta sanar da ita cewa mutanen da aka kama ne suka jagoranci manyan jami'an sojoji zuwa Angwan Loyo da ke gefen digar jirgin kasa, wurin da rijiyar da suka jibge gawar babbar sojar ta ke.

Masu laifin sun daddatsa jikin marigayiyar tare da saka ta a cikin wata babbar jaka kafin su wulla ta a cikin rijiyar.

Manjo Umar Shuaibu, jami'in hulda da jama'a a kwalejin horon manyan sojoji, bai amsa sakon da jaridar Daily Trust ta aika masa ba domin jin ta bakinsa a kan faruwa lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel