Wata sabuwa: An fara zaman sulhu bayan sabon rikici na kokarin barke wa a jihar Zamfara

Wata sabuwa: An fara zaman sulhu bayan sabon rikici na kokarin barke wa a jihar Zamfara

An shiga halin zaman dari-dari a masarautar Gwalli a karamar hukumar Gunmi da ke jihar Zamfara sakamakon nuna yatsa da aka fara yi a tsakanin kabilun Hausawa da Fulani da ke zaune a yankin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito ranar Lahadi.

Wata majiya da ke da masaniya a kan abinda ke faruwa ta sanar da jaridar cewa an fara samun rashin jituwa a tsakanin Hausawa mazauna Gwalli da wasu Fulani makiyaya da suka yi hijira zuwa yankin daga karamar hukumar Shinkafi ko Birnin Magaji a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari.

"Gwamnatin baya ta umarci makiyayan da su bar yankin bayan rigingimu tsakanin makiyaya da manoma sun yi tsanani a jihar Zamfara.

"Gwamnatin Abdulazizi Yari ta rubuta takarda zuwa masarautar Gunmi da karamar hukuma da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro tana mai umartar a tashi makiyayan daga yankin, bisa zargin cewa zasu iya kasancewa daga cikin batagari.

"Bayan makiyayan sun yi hijira zuwa yankin, sai suka fara sayen kadarori, musamman gonaki da filaye, ta hannun masu unguwa. Bayan sun fara aiki a gonaki da filayen da suka saya ne sai sako ya zo daga sama a kan su bar yankin.

"Wasu batagari daga cikin mazauna yankin sai suka fake da umarnin da gwamnati ta bayar a kan makiyayan, suka fara mayar da kadarorin makiyayan mallakarsu bayan makiyayan sun yi hijira zuwa jihar Kebbi," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: IBB ya aika muhimmin sako ga 'yan kabilar Igbo a kan fafutikar son a raba Najeriya

Majiyar ta bayyana cewa dawowar da makiyayan suka fara yi yankin ne yasa jama'ar da suka mallake musu kadarori suka shiga halin damuwa da fargaba saboda sun san cewa sun dawo ne domin daukan fansa.

Sai dai, yanzu haka gwamnatin jihar Zamfara a karkashin sabon gwamna, Bello Matawalle, ta gaggauta shiga tsakani tare da fara yin sulhu a tsakanin makiyayan da Hausawa don ganin cewa ba a kara samun barkewar wani rikici a jihar ba.

Wani mazaunin yankin mai suna Hassan Idris ya ce jami'an 'yan sanda sun gaggauta shiga lamarin kuma al'amura sun koma daidai don yanzu haka mutanen da suka gudu sakamakon zuwan makiyayan, sun dawo gari.

Shi ma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo, ya jagoranci jami'an tsaro zuwa fadar sarkin Gunmi, Alhaji Hassan Lawal, domin dora wa a kan zaman sulhu da gwamnatin jihar ke yi da 'yan bindiga da sauran masu tayar da kayar baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel