A yanzu mata na iya yawo ba riga a wasu jihohin Amurka guda 6

A yanzu mata na iya yawo ba riga a wasu jihohin Amurka guda 6

Wata kotun tarayya a kasar Amurka ta sanar da hallatawa mata a jihohin kasar shida yawo ba riga a bainar jama’a.

Kamar yanda jaridar Washington Times ta rahoto, kotun daukaka kara ta soke karan haramta wa mata yawo ba riga, wanda hakan yana nufin mata a halin yanzu suna iya bayyana sassan jikinsu a jihohin Colorado, Wyoming, New Mexico, Oklahoma, Kansas da Utah ba tare da fuskantan hukunci ba.

Birnin Fort Collins, Colorado ta yanke shawaran kawo karshen yakin muhawaran ba tare da kalubalantar hukuncin kotun tarayyar ba.

Kotun ta jadadda cewa haramtawa mata yawo ba riga zai zama “tauye masu hakki wanda ya saba yancin kundin tsari."

KU KARANTA KUMA: Wata tsohuwa ta shiga tasku bayan kamata da laifin siyar da wayan sata

A baya jami’an yankunan sunyi ikirarin cewa hukuncin kotun na nufin cewa mata zasu “dunga yawo a gaban makarantu ko wuraren wanka na zamani ba tare da rufe jikinsu ba."

Sai dai kuma, kotun daukaka karan a baya ta riki hukuncin mai shari’an dake ganin haramta hakan ya kasance cin zarafi.

Saboda wannan hukuncin, yanzu mata za su iya bayyana kirjinsu a bainar jama’a a jihohin shida kamar yanda aka rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel