Gwamna Badaru ya nada mashawarta na musamman guda 15 a Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya nada sabbin mashawartan gwamnatin sa na musamman guda 15 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A yayin da ya zuwa yanzu gwamna Badaru bai kafa sabuwar majalisa ba, wannan shi ne babban nadi da yayi tun bayan karbar rantsuwar sabuwar gwamnatinsa a wa'adi na biyu da aka gudanar a watan Mayun 2019.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sako na kunshe ne cikin wata sabuwar sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Adam Abdulkadir Fanini ya gabatar a yau Litinin 23 ga watan Satumban 2019.
Jerin sabbin hadimai da gwamnan ya nada a matsayin mashawartan sa na musamman sun hadar da;
Alhaji Yahaya Muhammad - Harkokin majalisar dokokin jihar
Mujitafa Saleh Kwalam - Harkokin Addini da assasa shari'a
Alhaji Ibrahim Isma'il - Karatun yaki da jahilci da makarantun gaba da sakandire
Jamilu Amaryawa - Harkokin Tsaro
Muhammad Mukhtar Zannan Kazaure - Haraji da Hannun jari
Garba Halilu - Tsare-Tsare
Buba Nasara - Kula da sanya idanun lura kan ayyuka
Sabi'u Musa - Ma'adanan ruwa da tsaftar zamantakewa
KARANTA KUMA: Cutar daji ce ta kashe Robert Mugabe - Mnagagwa
Ahmed Muhammad Babura - Harkokin Siyasa
Muntari Muhammad Birniwa - Ayyukan ci gaba
Tijjani Inuwa Tashi - Kasafin kudi
Bala Sule Kila - Harkokin Ma'aikatar Kurmi
Hamza Muhammad Hadejia - Harkokin inganta jin dadin Al'umma
Abbas Mujaddadi - Harkokin Tallafi
Bako Amaryawa - Harkokin Makiyaya da Manoma
Ibrahim Suleiman Gwiwa - Ayyukan samar da wuta ta hasken rana.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng