Raba Najeriya: IBB ya aika muhimmin sako ga 'yan kabilar Igbo

Raba Najeriya: IBB ya aika muhimmin sako ga 'yan kabilar Igbo

- Tsohon shugaban kasar Naeriya a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya shawarci 'yan kabilar Igbo da su zauna lafiya da sauran kabilun Najeriya

- IBB ya bukaci 'yan kabilar Igbo su cigaba da zamansu a lungu da sakon Najeriya domin cigaba da gudanar da harkokinsu da sauran kabilun Najeriya

- Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ba zata yarda ta tsage gida biyu ba.

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Ibrahin Badamasi Babangida (IBB), ya bukaci 'yan kabilar Igbo da su cigaba da bayar da gudunmawarsu wajen gina Najeriya domin tabbatar wa da jama'a cewa suna da muhimmanci ga kasa.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban kasar ya yi wannan kira ne ranar Asabar, 21 ga watan Satumba, yayin da ya karbi bakuncin wakilan 'yan kabilar Igbo (IDA) daga jihohin arewa 19, wadanda suka ziyarce shi a Abuja domin taya shi murnar cika shekaru 78.

IBB ya ce babu wani lungu da sako a Najeriya da kasuwanci bai kai 'yan kabilar Igbo ba, tare da bayyana su a matsayin masu tarbiyar kasuwanci.

DUBA WANNAN: Matatun man fetur 3 da zasu fara tace mai a mulkin Buhari - NNPC

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wakilan majalisar IDA sun kai wa IBB ziyarar ne bisa jagorancin shugabansu, Cif Chikezie Okezie da kuma shugaban 'yan kabilar Igbo na Minna, Eze Pampas Wahiwe.

Kazalika, ya yi gargadin cewa babu wani banbancin kabila, addini ko kuma na siyasa da zai sa Najeriya ta rabu gida biyu.

A nasa bangaren, Okezie ya yi addu'ar Allah ya kara wa IBB karfin jiki da kaifin basira domin ya cigaba da bawa Najeriya shawara a kan yadda zata shawo kan kalubalen da take fuskanta.

"A matsayinka na dattijo, Njeriya na matukar bukatar shawarwarinka a irin wannan lokaci da ake matukar bukatarsu," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel