Sojojin Najeriya sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram 7, jerin sunayensu

Sojojin Najeriya sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram 7, jerin sunayensu

Dakarun sojin Najeriya da na hadin gwuiwarkasashen gefen tekun Chadi (MNJTF) sun kashe a kalla kwamandojin kungiyar Boko Haram 7 a yankin tekun Chadi.

A wani jawabi rundunar soji ta fitar, kakakin rundunar sojojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya ce, "mun yi luguden wuta a wasu maboyar mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP a yankin Tumbus da ke gefen tekun Chadi, kuma mun kashe da dama daga cikinsu da suka hada da manyan kwamandojinsu.

"Sahihan bayanan sirri da muka samu daga cikin mambobin kungiyar da yanzu haka ke yin hijira zuwa kasar Sudan da kasar Afrika ta Tsakiya (CAR) sun tabbatar da cewa dakarun soji na MNJTF sun kashe a kalla manyan kwamandojin kungiyar guda bakawai.

"Kwamandojin da dakarun soji suka kashe sune: Abba Mainok, Bukar Dunokaube, Abu Kololo, Abor Kime (wanda ana zargin ya shigo kungiyar ne ta hannun ISIS domin bayar da horo, kasancewarsa balarabe), Mann Chari, Dawoud Abduolaye (dan asalin kasar Mali) da Abu Hamza.

"Dukkan wadannan mutane sun kasance kwamandoji da ke jagorantar mayakan kungiyar Boko Haram a yankin Tumbus kafin dakarun soji su hallaka su.

"Duk da ba lallai sunayen da aka bayar su kasance sunansu na gaskiya ba, duk da hakan, ba kankanuwar nasara muka samu ba a kokarinmu na karkade birbishin 'yan ta'adda da ke yankin.

"Amma duk da hakan, mu na kokari wajen ganin mun samu sahihan bayanai a kansu, musamman sunayensu na gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel