Shaidan ne ya sanya ni kashe dan kishiyata – Inji Harela Uba

Shaidan ne ya sanya ni kashe dan kishiyata – Inji Harela Uba

Wata mata yar shekara 22 mai suna Harela Uba ta amsa laifin kashe dan kishiyarta jariri dan kwana uku, a yankin Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Ta fada ma Northern City News a garin Minna, a ranar Alhamis, 19 ga wata Satumba, cewa shaidan ne ya tirsasata kashe dan kishiyarta da maganin kashe kwari wanda aka fi sani da ‘Ota Pia-Pia’.

An tattaro cewa mijin mai laifin wanda aka ambata da suna Saidu Uba na kauyen Shakodna ne ya kai ma yan sanda rahoto kan lamarin.

Ya fada ma yan sanda cewa amaryarsa Fa’iza ta shiga ban daki ta kuma bar jaririnta dan kwana uku a dakinta.

Saidu ya bayyana cewa a lokacin da mai jegon ta dawo daki, sai ta gano kumfa na fita daga bakin jaririn inda a gurguje ta tafi da shi Babban Asibitin da ke Kuta inda likitan ya tabbatar da mutuwar jaririn.

A wata hira da manema labaranmu, Harela wace ta kasance dauke da tsohon cikin wata takwas tace shaidan ne ya tursasa ta kashe yaron kishiyarta.

KU KARATA KUMA: Toh fah: Kungiyar CAN ta zargi El-Rufai da shirin rushe wata babbar coci mafi tsufa a Zaria

Yayin da yake magana akan lamarin, Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Muhammad Abubakar yace yayin binciken, Harela ta furta cewa ta tilasta diyarta yar shekara bakwai mai suna Khadija baiwa jaririn ‘pia-pia’.

Abubakar yace tuni aka gurfanar da mai laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel