Allah ka bamu mata na gari: Bayan shafe shekara 10 yana wahala da yaron tun yana jariri har ya girma, mahaifin ya gano cewa ashe yaron ba nashi bane

Allah ka bamu mata na gari: Bayan shafe shekara 10 yana wahala da yaron tun yana jariri har ya girma, mahaifin ya gano cewa ashe yaron ba nashi bane

- Bayan jimawa yana ta kokwanto akan wani yaron da aka bayyana masa cewa nashi ne na tsawon shekara 10, yanzu ya gano gaskiya

- Likitoci sun bayyana masa cewa ba shi bane ainahin mahaifin yaron, yayin da shi kuma ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa akan wannan lamarin

- An wallafa labarin mutumin a shafukan sada zumunta inda kuma mutane suka yi ta raddi akan lamarin

Labarin wani mutumi da aka wallafa da ya tsinci kanshi a cikin wani mawuyacin hali ya yadu a shafukan sadarwa. Mutumin yana da yaro dan shekara 10, amma kuma har yaron ya girma bai yadda cewa danshi bane, hakan ne yasa ya nemi likitoci su bayyana masa gaskiyar lamarin.

Abinda ake gudu ya faru domin kuwa likitocin sun bayyana masa cewa yaron nan dai ba dan shi bane na cikin shi. Sai dai kuma wannan labari da aka bayyana masa bai yi masa dadi ba domin kuwa yana son yaron matuka, kuma ya san wannan labari shine zai yi sanadiyyar kawo rashin zaman lafiya a gidansa.

Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna @AdvBarryRoux shine ya wallafa labarin a shafinsa, inda ya bayyana lamarin mutumin, hakan yasa mutane da yawa suka dinga raddi suna bayar da shawarwari dangane da lamarin ga mutumin.

KU KARANTA: Wannan abin dariya da yawa yake: Bidiyon yadda wasu 'yan sanda suka dinga bawa hammata iska a bainar jama'a

Da yawa daga cikin mutanen sun nemi mutumin yayi shiru da bakin shi kamar babu abinda ya faru domin kada hakan ya kawo karshen soyayyar dake tsakaninsa da yaron.

Haka kuma akwai wasu mutanen da suka nemi ya dauki matar tashi ita ya kaita a gwada ta a asibiti ya gane yanayin da take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel