Mijin Aisha Zakari matar da take tsorata gwamnan Kebbi ta wayar salula ya tona asirin asalin abinda ya faru

Mijin Aisha Zakari matar da take tsorata gwamnan Kebbi ta wayar salula ya tona asirin asalin abinda ya faru

- Bayan kama Aisha Zakari wacce hukumar DSS ke zarginta da kiran gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu a waya ta tsorata

- Yanzu haka mijinta ya fito ya tona asirin ainahin abinda ya faru, yayi bayani tun daga ranar da aka kama su har zuwa ranar da aka bayar da belinta

- Yace sai da suka shafe kwanaki goma sha uku a ofishin DSS ba a sanar da su laifin da suka yi ba kuma ba a bari sun ga 'yan uwansu ba

Bayan kama Aisha Zakari wacce ake zarginta da kiran gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu a wayar salula tana tsorata shi, yanzu haka mijinta ya fito yayi bayani dangane da abinda ya faru.

A lokacin da mijin nata yake magana da manema labarai, ya bayyana cewa: "Ranar 1 ga watan Satumbar nan, muna cikin gida da misalin karfe 12 na dare ana ruwan sama, kawai sai muka ji ana buga mana gida ana cewa a bude DSS.

"To kuma kun san yanayin matsaloli na tsaro na kasar mu, mu mun san babu wanda yayi laifi a cikin, sai muka fara shakkafr budewa saboda muna tsoron ko ba su bane, cikin karfi suka balle kofar gidanmu suka shigo da bindigogin su.

"Bayan shigowar su suka tara dukkan mu a tsakiyar daki suka ce duka mu basu wayoyin mu, ni kuma nace musu ni ba koshin lafiya ne dani ba, suka ce su ba barayi bane, basu ce mini ainahin ga abinda ya kawo su ba, sai suka daukeni nida babban dana da matata suka wuce damu ofis dinsu suka gaya mana cewa wai suna bincike ne.

KU KARANTA: To fah: Kasar Afrika ta Kudu ta zama ta daya a cikin jerin kasashen da suka fi arziki a nahiyar Afrika

"Da suka fito damu daga gida cikin daren nan na iske jami'an DSS kimanin 20 sun kewaye ko ina na gidan mu da bindigogi, haka suka dauko har muka kawo birnin Kebbi da karfe biyar na asuba, har zuwa karfe 10 na safe duk cikin mu babu wanda ya san abinda muka yi, amma dai sun kawo mana abinci munci.

"Bayan sun yi mini wasu tambayoyi na basu amsa, basu kara ce mini kala ba, muna wurin nan na tsawon kwana goma sha uku, babu wani wanda nake gani ko wanda na sani, babu wani dan uwana da yake zuwa wajen, an hana ni ganin kowa, an kuma karbe mini wayoyi na.

"Kuma ita matata zarginta ake yi har yanzu basu da wata hujja, kuma duk wanda yake zargin mutum shine ya kamata ya kawo hujja.

"Saboda haka muna godiya ga Allah da yasa kotu ta bayar da belinta, yanzu zamu je mu jira har zuwa ranar da suka ce mu dawo kotu muji kuma me zasu ce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng