Wata mata ta watsa ma yaro dan wata 10 ruwan zafi

Wata mata ta watsa ma yaro dan wata 10 ruwan zafi

Wata kotun Majistare da ke zama a Zaria, jihar Kaduna, ta tsare wata matar aure, Misis Nnennaya Edmond, a gidan yari kan zargin watsama wata mata mai goyo da danta mai watani 10 ruwan zafi.

Matar na fuskantar tuhume-tuhume biyu na aikata laifi da haddasa rauni a jikin Gloria Cyril da danta mai watanni 10, Bright Cyril.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa daga mai laifin har mai karan na zama ne a gida guda a yakin cocin ECWA da ke Wusasa, Zaria, jihar Kaduna.

Mai shari'a, Mista Abubakar Aliyu-Lamido, yayi umurnin cewa a tsare mai laifin a gidan yari sannan ya dage zaman zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, domin mai karan ta gabatar da shaidu.

Da farko, dan sanda mai kara, Sufeto Mannir Nasir, ya fada ma kotu cewa a ranar 10 ga watan Satumba, da misalin karfe 1:00 na dare, wata Mary Ijeoma ta kai rahoton lamarin ofishin yan sanda da ke Danmaaji.

Ya bayyana cewa Ijeoma ta zargi wacce ake kara da zuba ma yarta Gloria da jikanta mai watanni 10, Bright ruwan zafi.

Dan sandan ya kara d cewa wacce ke karan ta yi baynin cewa hakan ya haddasa rauni a jikin uwar da danta inda aka yi gaggawan kai su asibitin St Luke, Wusasa, domin jinya.

Ya bayyana cewa laifin ya saba ma sashi na 223 da 216 na dokar 2017.

KU KARANTA KUMA: Kaho mai tsawon inci 4 ya fito a kan wani mutum bayan ya yi hatsari

Sai dai wacce ake zargin bata amsa laifin tuhumar da ake mata ba.

Daga nan sai dan sanda, ya nemi kotu ta dan dage karan na dan gajeren lokaci domin ya gabatar da shaidu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel