Hukumar INEC ta shiga damuwa kan yiwuwar barkewar rikici a lokacin zaben gwamnan Kogi

Hukumar INEC ta shiga damuwa kan yiwuwar barkewar rikici a lokacin zaben gwamnan Kogi

Kwamishinan zabe na jihar Kogi, Farfesa James Apam, a ranar Talata, 17 ga watan Satumba ya nuna damuwa akan yiwuwar barkewar rikici a lokacin zaben gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, a jihar.

Apam ya bayyana hakan ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Lokoja.

Ya bayyana cewa a karo da dama hukumar INEC ta shirya gudanar da zabe na gaskiya sannan kuma a koda yaushe tana daukar matakan da ya kamata don tabbatar da zabe na gaskiya da amana, kawai sai azo a tarwatsa shi da rikici.

Kwamishinan zaben ya bayyana cewa hukumar na da niyan gyara matsalolin da aka gane a zabukan da suka gabata a zabe mai zuwa.

Apam ya yi kira ya iyaye musamman mata da su taimaka wajen yiwa yaransu magana akan guje na rigima, inda ya kara da cewa idan har babu rikici, toh mutane za su fito sosai a lokacin zabe sannan shirin zai kasance mai sauki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya rushe kwamitin shugaban kasa kan kwato kadarorin gwamnati

Kwamishinan zaben ya kuma bukaci masu zabe da su kimtsa kansu yadda ya kamata a lokacin zaben domin saukaka komai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng