Ga jerin hanyoyi 5 da mutum zai bi don guje ma tsufa mai rikitarwa

Ga jerin hanyoyi 5 da mutum zai bi don guje ma tsufa mai rikitarwa

Masu hikimar zance sunce tsufa labara ne, don haka idan har mutum na son ya tsufa da karfin shi ba tare da wahala ba, ya zama dole ya lazumci yin wasu abubuwa da zaran ya kai shekarun gangara.

Wadannan abubuwa kuwa da za su taimaka masa wajen kasancewa cikin koshin lafiya sun hada da; cin lafiyayyenn abinci mai gina jiki, guje ma yin kuskure wajen shan magunguna, kula da matsayin lafiya akan lokaci, zuwa neman shawarwari a wajen likitoci da kuma yawan motsa jiki.

Babu shakka kula da wadannan abubuwa 5 za su taimaka matuka wajen inganta tsufan mutum.

1. Cin lafiyayyen abinci

Cin abinci masu gina jiki na da matukar muhimmanci ga mutumin da girma ya fara zuwa mai. Da zaran mutum ya fara tsufa akwai wasu abinci da ya zama dole ya kula da cinsu domin suna iya zama masa matsala. Sannan mutu ya kula da cin abinci masu gina jiki, babu shakka hakan zai taimaka wajen inganta tsufan mutum ta yadda ba zai tagayyara ba.

2. Mutum ya guji yin kuskure wajen magani

Tabbass magunguna na taimakawa wajen magance matsalolin da suka shafi lafiya sannan yana taimakawa sosai wajen tsawaita rayuwar mutum cikin koshin lafiya. Sai dai kuma idan ba a yi amfani da magani yadda ya kamata ba yana iya haifar da matsala. Don haka bin ka’idar magani na da matukar tasiri wajen barin mutum ya kasance cikin koshin lafiya.

KU KARANTA KUMA: Za mu hukunta wadanda suka fallasa wasika kan bayanan asusun manyan jami’an gwamnati - NFIU

3. Kula da matsayin lafiya

Yana da matukar muhimmanci mutum yayi aiki tare da likitocinsa wajen kula da matsayin lafiyarsa musamman idan mutum na fama da wasu cututtukan zamani kamar irin ciwon siga da hawan jini. Mutum ya nemi sani kan magungunan da ya kamata yayi amfani da su wajen magance matsalolin.

4. Zuwa yin gwaje-gwaje

Yana na kyau ga mutumin da girma ya fara zuwa masa, ya dunga yawan zuwa duba lafiyarsa akai-akai ba wai sai an jira wata matsala ta kunno kai ba. Da zarann mutu ya ji alamu da bai gane ba toh ya garzaya a duba shi.

5. Motsa jiki

Yawan motasa jiki na sa mutum ya kasance cikin karfi da lafiya a koda yaushe. Maimakon zama waje guda mutum na iya jan kafa da wasu launuka na motsa jiki, ta haka ne mutum zai zamo cikin koshin lafiya a koda yaushe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel