Ba mu kama mutum haka nan ba tare da bin ka’idoji ba Inji EFCC

Ba mu kama mutum haka nan ba tare da bin ka’idoji ba Inji EFCC

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta sha alwashin maganin duk wani nau’i na rashin gaskiya a kasar nan. Shugaban hukumar ne ya bayyana wannan.

EFCC ta bayyana niyyar ta na ganin an daina sata a Najeriya ne a wajen wata hira da da aka yi da shugaban hukumar a wani babban gidan rediyo Garin Ilorin da ke jihar Kwara mai lamba 103.5.

Hukumar ta bayyana irin nasarorin da ofishin ta na shiyyar Ilorin ya samu kawo yanzu inda su ka yi nasarar sanadiyyar daure mutum 26 daga lokacin da ta fara aiki a farkon 2019 zuwa yau.

Isiyaku Sharu wanda ke shugabantar hukumar EFCC na yankin Ilorin da kewaye ne ya shaida wannan a Ranar Asabar 14 ga Watan Satumban 2019, lokacin da ya yi hira da ‘yan gidan rediyon.

Mista Sharu ya fara da cewa:

“Sashe na 7 na dokar kafa EFCC, ta bamu dama na musamman da za mu iya gudanar da bincike har mu gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifin satar kudi ko yi wa tattalin arziki barazana.”

KU KARANTA: Gwamna zai nada mutum 800 domin su rika ba shi shawara

Babban jami’in hukumar ya kare cewa ba su kama mutum hakanan kurum su tsare sannan kuma ya jero irin nasarorin da su ka samu a cikin watanni kusan bakwai da su ka soma aiki a shekarar nan.

Ya ce: “Mu na kokarin ganin mun yi aikin mu yadda ya dace, domin mu kwararru ne. Ba mu kama mutum mu tsare ba tare da mun bin doka ba. Mu na tattara hujjoji da shaidu kafin mu damke mutum.”

Sharu ya yi kira cewa: “Ina so in yi amfani da wannan dama domin kira ga jama’a su cigaba da bamu hadin kai wajen ganin mun yi maganin sata domin wannan yaki ya rataya ne a kan wutan kowa."

Jami’in ya kara jawabinsa da cewa: “Iyaye su kula da ‘Ya ‘yansu, domin su ne manyan gobe.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel