Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka yayin hira a gaban talabijin

Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka yayin hira a gaban talabijin

Jiya ne mu ka ji labari cewa babban ‘dan kwallon Duniya Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka lokacin da ake hira da shi a gaban talabijin a wani shiri da yayi da Piers Morgan kwanakin baya.

Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye a lokacin da aka bijiro masa da wani faifen bidiyo na Mahaifinsa. Ronaldo ya rasa Mahaifinsa ne a dalilin cutar hanta lokacin yana da shekaru 20.

‘Dan kwallon na Juventus ya kama rusa kuka ne yayin da ake hirar bayan da ya ga Marigayi Jose Dinis Aveiro a wani bidiyo da bai taba gani ba a da. Za a haska cikakkiyar hirar ne gobe Talata.

Ronaldo ya yi kuka ne a sanadiyyar tuna cewa Mahaifinsa bai taba ganin duk irin nasararorin da ya samu a rayuwa ba. ‘Dan wasan na Juventus ya zama Gwarzon shekara har sau 5 a Duniya.

KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya kama hanyar doke wani babban tarihin Duniya

An nunawa Cristiano Ronaldo wani bidiyo ne da Mahaifinsa ya ke magana yayin da shi yake jingine a jikin kofa. Ronaldo ya na kuka yake cewa bai taba ganin wannan bidiyo a Duniya ba.

Bayan Ronaldo ya gama kukan ya ke cewa: “Ina tunanin hirar ta na da ban dariya, ban yi tunanin zan yi kuka ba. Ban taba ganin wannan hotunan ba. Kuma ban taba sanin Mahaifi na sosai ba.”

‘Dan wasan ya kara da cewa: “Mahaifina Mashayi ne. Ban taba yin magana da shi ba, kamar yadda kowa yake hira. Abin da wahala.” Ronaldo ya rasa Mahaifin na sa ne a tsakiyar shekarar 2004.

"Dangi na, Mahaifiyata, ‘Yanuwa na, Hatta karamin Yaro na sun ga nasarar da na samu a rayuwa. Amma Mahaifina bai taba ganin komai ba. Amma… Ya mutu cikin kuruciyarsa.” Inji Ronaldo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel