Shehu Sani: Najeriya ta gaza kai labari a tsare-tsaren harkar noma na fita da doya da burodin rogo

Shehu Sani: Najeriya ta gaza kai labari a tsare-tsaren harkar noma na fita da doya da burodin rogo

Tsohon Sanatan jam’iyyar APC, Shehu Sani, ya fito ya soki manufofin gwamnatocin Najeriya na harkar gona. Shehu Sani ya caccaki gwamnatin Jonathan da ta shugaba Buhari ne a kaikaice.

Shehu Sani yake nuna cewa tsarin da gwamnatin Najeriya ta taba kawowa na yin burodi daga rogo bai kai ko ina ba. A lokacin mulkin Jonathan ne gwamnati ta kawo tsarin yin burodin rogo.

Haka zalika Sanatan ya caccaki yunkurin da gwamnatin kasar ta yi na fita da doya daga Najeriya zuwa kasashen ketare. Audu Ogbeh ne ya kawo wannan shiri a lokacin yana Ministan gona.

Daga cikin matsalolin da aka samu wajen fita da doyar zuwa kasashen etare shi ne rashin girman ‘ya ‘yan doyan da ake nomawa. A karshe dai lamarin ya shiririce kuma ba a sake bi ta batun ba.

KU KARANTA: Wutar lantarki za ta dawwama a Najeriya nan da 2023

Kwamred Sani har wa yau, ya caccaki rufe kan iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya ta yi. Yanzu haka dai an dauki tsawon makonni da rufe wasu daga cikin iyakoki saboda wasu dalilai.

‘Dan majalisar ya kuma koka game da yadda kasar Argentina ta ke cin ribar rikicin da ake yi tsakanin kasar Sin da Amurka inda yace yanzu Argentina ta dage wajen shigo da waken suya.

Sanatan ya fito ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Tuwita a karshen mako. Sani ya wakilci Kaduna a majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019 kafin ya sauya sheka ya kuma rasa kujerar.

Duk a shafin Sanatan, an ji ya na yabawa matakin da shugabannin ECOWAS su ka dauka na hada kudi Dala biliyan guda domin kawo karshen ‘yan ta’addan da su ka addabi Nahiyar Afrika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel