Tsohon mijina ya yi min asiri, babu wanda ya kara cewa yana so na tun bayan rabuwar mu

Tsohon mijina ya yi min asiri, babu wanda ya kara cewa yana so na tun bayan rabuwar mu

Wani miji, Akintayo Kalejaye, da matarsa, Funmilayo Kalejaye, sun bayyana a gaban wata kotun gargajiya da ke Mapo a garin Ibadan, jihar oyo, domin neman kotun ta basu takardun shaidar cewa aurensu ya mutu shekaru biyu da suka gabata.

Miji da matar na yi wa juna zarge-zarge masu nauyi da suka hada da cin amanar aure, rashin ganin girma juna, da kuma nuna wa jutansu keta da mugunta a bayyane.

Da take bayyana dalilanta na amincewa ta gurfana a gaban kotun domin neman shaidar mutuwar aurensu, Funmilayo ta shaida wa alkalin kotu cewa, "miji na ya wulakantar da ni da 'ya'yan mu biyu da muka haifa tare, bai damu ba ko mu mutu ko mu rayu.

"Ba ya iya sauke nayin mu da ya rataya a wuyansa, amma a hakan ya je ya kara aure a wani wurin ba tare da sani na ba, a yayin da gidan da muke ciki ma ni ce ke biyan kudin haya.

DUBA WANNAN: An sace lakcara, matasa biyu da wasu mutane 5 a kwaryar birnin Abuja

"Akintayo shaidanin mutum ne mai mugun hali, saboda kafin na bar gidansa sai da ya je wurin wani boka a Ijebu Ode yasa aka yi min asirin da maza za su daina sha'awa ta.

“Tun da na bar gidansa har yanzu babu wani namiji da ya taba cewa yana so na. Ina rokon wannan kotu ta tilasta wa Akintayo yasa a warware asirin da aka yi min ko na samu canji a rayuwata," a cewar Funmilayo.

Kazalika, Funmilayo ta zargi mijinta nata da neman mata barkatai, lamarin da yasa tuntuni alaka a tsakaninsu ta lalace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel