A daina auren Mata da yawa - Sarkin Anka ya gargadi masu karamin samu

A daina auren Mata da yawa - Sarkin Anka ya gargadi masu karamin samu

Sarkin garin Anka a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Alhaji Attahiru Ahmed, ya gargadi wadanda samun su bai taka kara ya karya ba a kan su kaurace wa auren mace fiye da daya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Basaraken na Arewan ya yi wannan gargadi a ranar Lahadi cikin fadarsa da ke garin Anka, ya ce aurace-auracen da ake kullawa a tsakanin masu karamin karfi ke kara jefa kasar nan cikin matsi na tattalin arziki da haddasa katutu na talauci.

Shakka babu, masu hangen nesa da dama sun fadakar tare da jan hankali a kan auren mace fiye da daya ga wadanda samun su bai da wani tasiri wajen kula da harkokin iyali da kuma dawainiyar rayuwarsu ta yau da kullum.

Alhaji Attahiru ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke rarraba wasu kayayyakin tallafi na dogaro da kai ga Mata wanda uwar gidan gwamnan Zamfara, Hajiya Aisha Bello Mutawalle, ta bayar a kananan hukumomin da suke shiyyar Zamfara ta Yamma da suka hadar da Anka, Bukkuyyum, Gummi, Maradun, da Talata-Mafara.

A kalamansa Alhaji Attahiru ya ce, "ma'aikatan da samun su bai wuce Naira 15,000 ba a kowane wata, auren mace fiye da daya ba nasu bane domin ba za su iya daukar nauyin iyalan su ba."

"Wannan lamari shi ke haddasa karuwar rashin samun ilimi musamman a tsakanin yara a sanadiyar gazawar iyayen su wajen daukar nauyin da rataya a wuyansu."

"Ya kamata mutane su rinka sara su na duban bakin gatari a yayin aure gwargwadon karfin samun su domin samun damar daukar nauyin 'ya'yansu ta fuskar ingataccen ilimi da kuma kyakkyawar dabi'a ta tarbiyantar da su."

A yayin da ya ke yabawa wannan goma ta arziki ta Hajiya Aisha, Sarkin ya kuma shawarci wadanda suka samu tallafi matar gwamnan da su yi tattalin arzikin da suka samu wajen dogaro da kai da kuma kula da iyalansu ta mafificiyar hanyar dace.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel