Kwana guda bayan harin Boko Haram, Gwamna Zulum ya ziyarci jami’ar Maiduguri
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, ya ziyarci jami’ar Maiduguri, kwana daya bayan yan ta’addan Boko Haram sun yi yunkurin kai hari a makarantar.
A yayin ziyarar, Zulum ya bayyana cewa ya umurci kwamishian ayyuka da ya fadada hanyar rowan da ke kewaye da makarantar ba tare da bata lokaci ba.
Zulum ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter, @GovZulum, jaridar Punch ta ruwaito.
“Na umurci kwamishinan ayyuka da yayi gaggawan kawo masu hake-hake domin su fadada hanyoyin ruwa da ke kewaye da jami’ar.
“Za kuma mu samar da kayayyaki ga jami’an tsaro domin zuba idanu sosai. Bari kuma na sake jadadda jajircewar gwamnatina wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutanenmu,” inji Zulum."
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jakadun Afrika ta Kudu sun iso Abuja domin tattauna zaman lafiya da Buhari
A baya Legit.ng ta rahoto cewa an shiga cikin wani hali na la-hau-la a daren jiya Lahadi, 15 ga Watan Satumba, 2019, inda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka nemi su kai hari a babban jami’ar tarayya da ke Maiduguri a Borno.
Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Sojoji sun yi namijin kokari wajen hana ‘yan ta’adda kai faramaki a jami’ar Maiduguri wanda aka fi sani da UNIMAID yayin da ake shirin gama zango.
Wadanda su ke kusa da makarantar sun tabbatar da cewa an ta ji barin bindiga daga yankin titin Maiduguri zuwa Bama. A daidai wannan bangare ne dakin kwanan ‘dalibai mata na jami’ar yake.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng