Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Hatsarin mota ya hallaka mutane 13 tare da jikkata wasu 11 a Nasarawa

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Hatsarin mota ya hallaka mutane 13 tare da jikkata wasu 11 a Nasarawa

Rahotanni sun kawo cewa mutane 13 sun rasa ransu sakamakon hadarin mota da ya afku a kusa da Unguwan Ciyawa da ke karamar hukumar Eggon na jihar Nasarawa a jiya Lahadi, 15 ga watan Satumba.

Kwamandan hukumar kula da hana afkuwar hadarurruka a jihar, Ismaila Kugu, ya bayyana cewa wadanda abun ya cika da su sun kasance manya 10 da kananan yara uku, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa wasu mutane 11 sun jikkata a hadarin.

Yace: “Mun kwashi wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu zuwa asibitin Nasarawa Eggon.

Yace hadarin ya afku ne tsakanin wata babbar mota mai lamba MSA 513 XA; da wata bas mai lamba BDG 530 SU, mallakatr kamfanin sufuri na jihar Benue da kuma wata bakar mota mai lamba RBC 45 AT.

KU KARANTA KUMA: Masu yi mani izgili a kafafen sada zumunta su na bani dariya – Inji Yemi Osinbajo

Wani idon shaida yace babbar motar da bas din sun kara da juna, sannan birki ya kwace inda bakar motar kuma ta shige su, sannan ta fada cikin wani rami da ke gefen hanya.

Wani matuki, Jibrin Gwamna, yace tsawon sa’o’i da dama, hadarin ya toshe hanyyar da ke sada Eggon, Akwanga da Lafiya, babban birnin jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel