Tirkashi: An sace tukunyan masai da aka kera da gwal a fadar Birtaniya

Tirkashi: An sace tukunyan masai da aka kera da gwal a fadar Birtaniya

Abun bakin ciki ya faru a fadar Blenheim yayinda wasu yan ta’adda suka sace sabon tukuyan masai na gwal da aka sanya wanda farashinsa ya kai Yuro miliyan 1 (£1million).

A cewar yan sandan Thames Valley, lamarin wanda ya afku a fadar da ke Woodstock, Oxfordshire, da misalin kare 5:00 na safe, ya haddasa bara sosai da kuma ambaliyar ruwa.

An sanya wa tukunyan masan wanda wani mai yin zane-zane na kasar Italiya Maurizio Cattelan ya kera suna “America” sannan an bayyana shi ne a mahaifar Winston Churchill a wannan makon.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Sokoto 2 kan zargin karkatar da albashin ma’aikata

Jaridar Mirror ta ruwaito cewa baki kan nemi izinin shiga wajen kafin lokaci. Sannan an nemi su mutunta tsarin minti uku da aka gindaya domin ba sauran mutane dammar amfani dashi.

Sai dai, yan sanda sunce sun kama wani dan shekara 66 da ke da nasaba da afkuwar lamarin.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasar Philippine, Rodrigo Duterte, ya nemi mutanen kasarsa da su harbi duk wani barawon dan siyasa da suka san yana sace musu dukiyar kasa, amma kuma kada su kashe.

Shugaban kasar mai shekaru 74, yace duk wani mutumin da ya ga wani dan siyasa ko mai mukami yana karbar cin hanci ko yana satar dukiyar kasa to ya harbe shi, shi kuma yayi alkawarin zai bawa mutumin kariyar da babu abinda zai same shi, amma kuma yayi gargadi kada ayi harbin da zai saka dan siyasar ya mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel