Bazan iya wannan masifar ba nima fita zanyi daga Kannywood wallahi - Teema Makamashi

Bazan iya wannan masifar ba nima fita zanyi daga Kannywood wallahi - Teema Makamashi

- Bayan kama Mawaki Nazir Ahmad Sarkin wakar San Kano, jarumai da yawa sun fito sunyi Allah wadai da wannan abu da hukumar tace fina-finai tayi

- Wannan yasa jaruma Teema Makamashi jakadiyar FKD ta wallafa wani bidiyo inda ta nuna bacin ranta game da wannan abu da yake faruwa a masana'antar

- Teema ta bayyana cewa ita ma za ta bi sahun abokanan sana'arta da suka fita daga kungiyar saboda irin abubuwan da suke faruwa a kungiyar

A irin kace nacen da ake ta faman samu dangane da kama fitaccen mawakin nan Nazir Ahmad Sarkin wakar San Kano, mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari da ya faru da mawakin.

Wannan dalili ne yasa Jaruma Teema Makamashi jakadiyar FKD tayi wani bidiyo cikin nuna alhini inda ta nuna bacin ranta akan kama Nazir din da aka yi har ta yi ikirarin ita ma ta kusa tabi sahun abokanan sana'arta da suka fice daga kungiyar shirya fina-finai ta Kannywood saboda ta gaji da abinda ke faruwa a masana'antar.

Ga abinda jarumar ta ce:

"Assalamu Alaikum, kamar dai yadda kuka sani sunana Teema Makamashi, yau kuma da abinda Kannywood ta wayi gari dashi kenan, ni sai yau nake ji wai an kama Nazir Sarkin waka, shugaban hukumar tace fina-finai a yiwa Nazir Sarkin waka adalci a sake shi.

KU KARANTA: To fah: A karon farko Jarumi Ali Nuhu yayi magana kan kamen da hukumar fina-finai take yi

"Wannan abu da ake yi ko ba dan siyasa bane za ace saboda siyasa ne, saboda mun zo mun shiga siyasa mun zake, sun zo sai raba kawunan mu suke su suna can suna samun kudade, mu munzo wajen da muke cin abinci a nan za a tsaya kullum ana fada, babu ranar da garin Allah zai waye ba ayi wani abu a Kannywood ba.

"Wallahi gaskiya na kusa na bar Kannywood, ba zan iya wannan masifar ba, a yiwa Nazir Sarkin Waka adalci a sake shi, duka 'yan kwankwasiyya ake ta kamawa, 'yan APC din basa laifi ne, tunda aka fara wannan abun ba a taba kama dan APC ba, an jera hotunan jarumai biyar ance za a kamasu, kuma duk 'yan PDP ne."

Haka shima Jarumi Ali Nuhu ya fito ya roki hukumar da tayi sassauci akan wannan lamari, inda ya roketa da ta yiwa jarumin adalci ta sake shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng