Kaso 80 na yan asalin Gombe na rayuwa cikin tsananin talauci – Gwamna Inuwa Yahaya

Kaso 80 na yan asalin Gombe na rayuwa cikin tsananin talauci – Gwamna Inuwa Yahaya

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kimanin kaso 80 na mutane miliyan 3.2 da ke jihar na rayuwa cikin tsananin talauci.

Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, 12 ga watan Satumba, a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar ci gaban arewa maso gabas.

A cewarsa adadin ya ninke kusan sau biyu sakamakon yawan hare-haren Boko Haram a jihohin da ke kwabtaka na Borno da Yobe.

Ya nemi goyon bayan hukuma da kuma jaddada shirin gwamnatinsa don ba da duk wani goyon bayan da hukumar ta NEDC ke bukata don cimma nasara.

A cewar gwamna, fiye da shekaru 10 da Boko Haram suka yi suna kai hare-hare da kuma kafa sansani ga tubabbun yan ta’adda ya saka jihar a hasara.

KU KARANTA KUMA: Sanata Musa ya koka kan wata babban matsala da ke ciwa al'ummar mazabarsa tuwo a kwarya

Da farko, Shugaban kungiyar NEDC, Paul Tarfa yace a cikin shekaru 10 na ta’addanci, kimanin rayuka 20,000 ne suka salwanta inda sama da mutane miliyan biyu suka fuskanci rashin muhalli da kuma hasaran gine-gine da hanyoyin cin abincin su.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Mungono, a jiya Alhamis, 12 ga watan Satumba, ya bayyana cewa ana shigo da muggan makamai cikin Najeriya ta iyakokin kasar.

Da yake magana a Lagas a wajen kaddamar da sabbin bindigogin jiragen ruwa biyu da hukumar kwastam na Najeriya tayi a wajen kera jiragen ruwan rundunar sojin ruwa, yace yan Najeriya da dama sun mutu sakamakon muggan makamai da ake fasa kaurinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel