Wata sabuwa: A tura sojoji mata su yaki 'yan ta'adda tunda mazan sun kasa tabuka komai - Aisha Buhari

Wata sabuwa: A tura sojoji mata su yaki 'yan ta'adda tunda mazan sun kasa tabuka komai - Aisha Buhari

- Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta bukaci hukumomin tsaro su bai wa sojoji mata dama a dama dasu a kasar nan

- Matar shugaban kasar ta ce idan har ana so a kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya to dole ne a cire banbanci tsakanin mace da namiji a gidan soja

- Aisha Buhari ta dora alhakin rashin samun nasara da ake akan 'yan ta'addan kasar nan da hana sojoji mata su fita su gwada bajintarsu a filin daga

A jiya Alhamis ne 12 ga watan Satumbar nan matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari, tayi kira ga hukumomin tsaro na kasar nan da su tura sojoji mata suyi yaki da matsalar tsaro a wasu jihohi na kasar nan.

Da take magana a wajen wani taro da hukumar tsaro take gabatarwa a kowacce shekara a Abuja, matar shugaban kasar ta dora alhakin matsalar tsaron da ake samu da rashin bawa sojoji mata su gwada bajintarsu a fannin tsaro.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna

Aisha Buhari wacce ta samu wakilcin mai taimaka mata ta musamman Dr. Hajo Sani, ta bayyana cewa idan har ana son samun cigaba a bangaren tsaro a Najeriya to dole ne a cire wariya tsakanin mace da namiji.

Haka shima da yake magana a wajen taron, shugaban ma'aikatan hukumar tsaro ta kasa Janar Gabriel Olonisakin ya ce hukumar soji ta sanya kashi 27.7 cikin 100 a fannin kawo zaman lafiya a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel