Shugaba Buhari yana ganawa da shugabanin TUC a Aso Rock

Shugaba Buhari yana ganawa da shugabanin TUC a Aso Rock

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 12 ga watan Satumba ya gana da sabbin shugabannin kungiyar 'Yan Kasuwa ta Najeriya (TUC).

The Nation ta ruwaito cewan an shiga taron ne misalin karfe 12.30 na rana a ofishin shugaban kasar da ke gidan gwamnati a babban birnin tarayya, Abuja.

Mr Quadri Olaleye na kungiyar FOBTOB ne ya zama sabon shugaban kungiyar 'yan kasuwan TUC.

Ya maye gurbin Bobboi Kaigama bayan wata yarjejeniya da aka cimma a karshen taron wakilai karo 11 da aka gudanar a Abuja.

An zabi Mr Olaleye domin jagorantan wata kwamitin mambobi 14 na masu rike da mukammai a kungiyar da za su tafiyar da harkokin kungiyar na shekaru uku masu zuwa gaba.

DUBA WANNAN: Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

Sauran shugabanin da aka zaba sun hada da Bola Audu na ASCSN a matsayin mataimakin shugaba na farko, Onyinkan Olasanoye a matsayin mataimakin shugaba na biyu sai Hygenius Chika Onuegbu a matsayin mataimakin shugaba na uku.

Saura sun hada da Muhammed Yunusa a matsayin ma'aji, Isaac Egbugara a matsayin sakataren kudi da sauransu.

Ministan Kwadago, Dakta Chris Ngige shima ya samu hallartan taron.

Har yanzu ba a kammala taron ba a lokacin wallafa wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel