Allah Sarki: Mansura Isah ta fashe da kuka yayin da take magana akan irin halin da 'ya'yan talakawa ke ciki

Allah Sarki: Mansura Isah ta fashe da kuka yayin da take magana akan irin halin da 'ya'yan talakawa ke ciki

- Tsohuwar fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, mata a wajen Sani Danja an hasko ta a wani bidiyo tana kuka akan irin halin da talakawa ke ciki

- Jarumar ta bayyana cewa babu abinda masu kudi da gwamnati ke yiwa talaka wanda zai samu sauki a rayuwarsa

- A karshe jarumar tA roki gwamnati da masu kudi su hada kai su samar da cigaba a bangaren ilimi koda yaran talakawa zasu samu sauki a rayuwarsu

Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta, ya bazu a duniya inda yake nuna tsohuwar jarumar wasan Hausa kuma mata a wajen fitaccen jarumi Sani Musa Danja, wato Mansurah Isah.

An nuno jarumar a bidiyon tana magana akan yadda rayuwar 'ya'yan talakawa ke ciki a wannan lokacin, inda saboda tsabar tausayi yasa tana cikin magana har kuka ya kwace mata.

Ga abinda tsohuwar jarumar take cewa a bidiyon:

"Shuwagabannin mu mai kuke yi? Kullum kuna rubuta kasafin kudi, kowacce shekara sai kun saki kasafin kudi, wannan kasafin kudin da ake yi ana bawa ma'aikatar ilimi kasonta, shin me ake yi da kudin da ake karba na ma'aikatar ilimi?

"Masu kudin mu basa taimakawa talakawa, gwamnati ma babu abinda ya dameta da talaka, idan kaga gwamnati na neman talaka to lokacin zabe ne ya karato.

"Mai yasa baza mu hadu mu taimakawa al'umma ba, mai yasa gwamnati baza ta tashi tsaye ta taimakawa mutane ba, koda ma ba a bamu hanya ba, ba a bamu wuta da ruwa ba, ya kamata ace koyaya ne mun samu ilimi mai inganci.

"Ya za'ayi ace mutum ya tafi neman ilimi babu wajen da zai zauna, babu rufi cikin zafin rana da datti haka zai zauna a kasa, mai gwamnati da masu kudi suke yi don taimakawa talaka, kada ku manta fa ranar gobe kiyama hakkinmu dake kanku sai Allah ya tambayeku.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Wani matashi ya roki Rahama Sadau tayi fim din batsa koda guda daya ne

"Ina rokon masu kudin mu ina rokon gwamnati da ku taimaka ku kawo gyara a wannan fannin."

Tsohuwar jarumar tana cikin magana kuka ya kwace mata ya zamanto dakyar maganar ta fita daga bakinta. Jarumar ta cigaba da cewa:

"Menene amfanin, shugaban kasa, ministan ilimi, kwamishina, gwamnoni, ciyamomi da kansiloli, babu wani abu da kuke yi, babu abinda muke gani sai zama cikin wahala da tashin hankali saboda kawai mun fito a cikin talauci, wanda kuma ba mune muka dorawa kanmu ba.

"Ya Allah ina rokonka ka gyara mana kasar mu Najeriya, ko mu da 'ya'yanmu bamu gani ba Allah kasa jikokin mu su gani, saboda halin da Najeriya take ciki abin takaici ne da tausayi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel