Allah ya kyauta: Wani matashi ya roki Rahama Sadau tayi fim din batsa koda guda daya ne

Allah ya kyauta: Wani matashi ya roki Rahama Sadau tayi fim din batsa koda guda daya ne

- Wani matashi ya roki Rahama Sadau da ta daure tayi musu fim din batsa koda guda daya ne

- Matashin ya bayyana hakan ne bayan ya ga wasu kayatattun hotunan ta masu daukar hankali

- Sai dai jarumar har yanzu bata ce masa uffan ba, inda mutane kuma suka yi masa caa da maganganu

Wani matashi mai amfani da kafar sadarwa ta Twitter mai suna 'Error Chachera' yayi batanci ga jaruma Rahama Sadau a shafinta na Twitter bayan ta wallafa wasu hotuna masu daukar hankali.

Matashin dai yayi magiya ga jarumar ne inda ya roketa da ta girman Allah da ta daure tayi musu fim din batsa koda guda daya ne.

Sai dai wani abin mamaki game da matashin shine, duk da dai cewa ba da ainahin sunanshi yayi amfani ba a shafin ba yayi amfani da suna 'Error Chachera', amma hoton sa sanye yake cikin kaya masu kamala kaftan da hula da ka ganshi kaga mutum mai kamala.

KU KARANTA: Kar ku damu ko kadan saboda har yanzu mune da nasara - Dino Melaye na rarrashin mabiyansa

Koda yake kai dai kaga mutum a riga amma baka san ainahin halayyarsa ba har sai yayi magana zaka samu ajin da zaka sanya shi. Domin kuwa wannan magana tasa ta jawo shan martani daga al'umma inda wasu kuma suke ta kyakyatawa kan maganar tasa.

Duk da dai cewa Rahama bata mayar masa da martani ba ko ta nuna cewa ta ga rubutun nasa, amma wasu daga cikin masu tsokaci sun bata laifi, inda suke cewa inda ace shigar kamala tayi da ba wanda zai mata irin wannan magana ta tozarci inda wasu kuma ke cewa dashi da itan duk kanwar ja ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng